Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Na Kara Kai Hare-hare a Jihar Arewa Mai Nisa ta Kamaru


Kwanaki hudu a jere 'yan Boko Haram suke kai hare-haren kunar bakin wake a jihar Arewa Mai Nisa dake kasar Kamaru inda aka gano maharan suna labewa ne da 'yan gudun hijira su aikata ta'adanci

Maharan na 'yan Boko Haram suna ta kai wasu hare-hare a wasu kauyuka da garuruwa cikin jihar Arewa Mai Nisa ta kasar Kamaru, jihar dake makwaftaka da Najeriya.

A wani kauyen dan kunar bakin wake ya kunce damarsa ya tada bam cikin tsakiyar jama'a nan take kuma mutane hudu suka sheka lahira kana sama da goma suka jikata.

Bayan harin an gano wani kuma dake kokarin tada nasa bam din kusa da wani barikin sojojin kasar Kamaru dake daf da kan iyaka da kasar Najeriya kafin ya aikata aika aika.

Mai ba kakakin ministan tsaro shawara ta bangaren tsaro a kan Boko Haram a Arewa Mai Nisa, Lawali Jika yace kamar akwai lauje cikin nadi. Injishi kwana uku ke nan da suka kama wani dan gudun hijra daga Najeriya yana shirin kai harin kunar bakin wake. Lamarin ya nuna masu cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun shiga 'yan gudun hijiran.

Yanzu gwamnatin kasar ta Kamaru ta kuduri aniyar yin bincike gida gida domin zakulo 'yan Boko Haram da suke fakewa cikin jama'a.

A saurari rahoton Garba Awal.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:51 0:00

Facebook Forum

Matsalar Tsaro A Zamfara

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Kamu A Auren Nupawa

Yadda Nupawa Suke Kamun Ango A Bikin Aure
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG