Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Kai Farmaki Kan Kurkukun Bauchi


Hukumomi sun ce sun shawo kan farmakin na wadannan 'yan bindiga amma majiyoyi sun ce maharan sun fasa wannan kurkuku sun saki dukkan fursunonin dake cikinsa.

Hukumomi a Najeriya sun ce wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kan wani gidan kurkuku inda ake rike da ‘ya’yan wata kungiyar ‘yan tsagera.

‘Yan sanda suka ce ‘yan bindigar sun bude wuta daidai lokacin da ake buda-baki talata, a kan gidan kurkukun garin Bauchi, inda aka dauki tsawon lokaci ana musanyar wuta a tsakaninsu da jami’an tsaro. Jami’ai suka ce daga baya sun samu nasarar shawo kan lamarin.

Ba a dai san irin rauni ko mace-macen da aka yi lokacin wannan dauki-ba-dadin ba. Wasu shaidu sun ce sun ga gawarwaki a wurin, sun kuma ga fursunonin da suka tsere.

Hukumomi suka ce sun yi imanin ‘yan bindigar ‘yan kungiyar Boko Haram ce kuma sun kai harin ne domin kubutar da membobinsu dake daure cikin wannan kurkuku su na jiran shari’a.

Wani ma’aikacin gidan kurkukun na Bauchi, ya shaidawa Muryar Amurka cewa ‘yan bindigar sun fasa wannan kurkuku, sun kuma saki dukkan fursunonin dake cikinsa.

XS
SM
MD
LG