Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Limami A Maiduguri


Gawarwaki na wadanda ake zaton 'yan Boko haram ne a kusa da wata motar 'yan sanda a Maiduguri, ranar 31 ga watan Yulin 2009, lokacin mummunan gumurzun da aka yi a tsakanin jami'an tsaro da 'ya'yan kungiyar.
Gawarwaki na wadanda ake zaton 'yan Boko haram ne a kusa da wata motar 'yan sanda a Maiduguri, ranar 31 ga watan Yulin 2009, lokacin mummunan gumurzun da aka yi a tsakanin jami'an tsaro da 'ya'yan kungiyar.

'Yan bindiga sun bude wuta suka kashe Imam Ibrahim Abdullahi mai sukar lamirin 'yan Boko Haram a kofar gidansa dake unguwar Bolori a Maiduguri.

Wasu 'yan bindiga a yankin arewa maso gabashin Najeriya sun bindige suka kashe wani sanannen Limami wanda yake sukar lamirin zub da jinin da tsageran addini suek yi.

Shaidu a unguwar Bolori dake Maiduguri, hedkwatar Jihar Borno, sun ce 'yan bindigar sun zo cikin wata motar jeep suka bude wuta a kan Sheikh Ibrahim Abdullahi a daidai kofar gidansa dake jikin wani Masallaci da misalin karfe 8 na daren jiya lahadi.

Babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin.

Sheikh Ibrahim Abdullahi sanannen mai sukar lamirin kungiyar nan ce ta Boko Haram wadda ta kaddamar da tayar da kayar baya a Maiduguri a shekarar 2009, inda aka kona wuraren ibada da ofisoshin gwamnati. An kashe mutane fiye da 700 a wannan fitinar.

Sojoji da 'yan sanda sun kai farmaki mummuna suka murkushe 'yan kungiyar a 2009, amma tun shekarar da ta shige ta 2010, kungiyar ta sake kunno kai inda ta yi ta kai hare-hare, mafi yawa a kan 'yan sanda.

XS
SM
MD
LG