WASHINGTON, DC —
Yawan hare-haren ta’addancin ‘yan kungiyar Boko Haram, da kuma rikice-rikicen kabilanci, tsakanin manoma da makiyaya,ya sanya ‘yan gudun hijira, ya haura dubu dari bakwai.
Kwamishinar kula da ‘yan gudun hijira ta Najeriya, Hadiza Sani Kan Giwa tace, “a kwai mata da yara da suka rasa mazajensu da iyayensu, akwai maza da suka rasa gidajensu da wuraren sana’ar, su, wasu kuma basu da lafiya, gwamnatin tarayya tana iyakacin kokarinta, na tabbatar da ganin cewa an inganta rayuwarsu.
‘Yan gudun hijirar dai nada ra’ayi daya, na fatan lamura su daidai ta a garuruwansu, domin su koma gida.
Rashin tsaro a yankuna da dama na Najeriya, na matukar illa ga ilimi, harkokin kiwon lafiya da tattalin arziki.
'Yan Gudun Hijirar Najeriya Sun Kai Dubu Dari Bakwai - 2'53"