Accessibility links

Yan Hamayya na Shirin Yin Gagarumar Zanga Zanga Yau A Misira

  • Grace Alheri Abdu

Wata mai zanga zangar kin jinin shugaba Mohamed Morsi

'Yan Hamayya suna shirin gudanar da zanga zanga yau lahadi da nufin neman shugaba Mohamed Morsi ya yi murabus

Hankali na kara tashi a Misira, inda ake shirin gudanar da gagarumar zanga zanga yau lahadi da nufin kira ga shugaban kasar Mohammed Morsi ya yi murabus.

Masu shirya zanga zangar sun bayyana jiya asabar cewa, sama da mutane 22 ne suka sa hannu a korafin dake kira ga shugaban kishin Islaman ya yi murabus, da cewa, adadin wadanda suka sa hannu a korafin alama ce cewa, jama’a sun juyawa mulkinshi baya.

Jiya asabar, dubban mutane suka taru a dandalin Tahrir dake birnin Alkahira yayinda ake shirin gudanar da zanga zangar.

A kalla mutane bakwai aka ce an kashe da suka hada da ba’amurke daya yayinda daruruwan mutane suka ji raunuka a fito na fiton da aka yi tsakanin masu goyon baya da wadanda suke adawa da Mr. Morsi a cikin wannan makon.

Tun farko jiya asabar, shugaba Barack Obama yace Amurka ta damu da yadda rikicin siyasa yake kara kamari a Misira.

Yayin wani taron manema labarai na hadin guiwa a Pretoria tare da takwaranshi na Afrika ta Kudu, shugaba Obama yace Amurka tana goyon bayan daukar matakin lumana na kawo canji a Misira.

Yace ina jin ya kamata kowanne bangare ya guji tashin hankali. Muna so muga masu hamayya da shugaba Morsi sun shiga tattaunawa kan hanyar ciyar da kasarsu gaba domin babu wanda yake amfana da rudamin da ake yi a kasar a halin yanzu.
XS
SM
MD
LG