Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan jam’yar Republican a majalisa suna matsawa fadar White House lamba


‘Yan jam’yar Republican a majalisa suna matsawa fadar shugaban kasa ta White House lamba ta fitar da faifan tattaunawa shugaba Donald Trump da darektan hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI James Comey da aka kora, idan an nadi tattaunawar.

Faifan tattaunawar zai warware kace na nace da ake yi kan ko Trump ya bukaci Comey wanda yake jagorantar binciken da ake gudanarwa kan shish-shigin da ake zargin Rasha tayi a zaben shugaban kasar Amurka da aka gudanar bara, ya dakatar da binciken da hukumar ke gudanarwa a kan wanda Trump ya fara zaba a matsayin mai bashi shawarwaci kan harkokin tsaro, Micheal Flynn. Trump ya kori Flynn sabili da yin karya a kan huldarsa da jakaden Rasha a Washington.

A bayanin da yayi gaban ‘yan majalisa makon da ya gabata, Comey ya bada bahasi cewa, yana jin Trump yana so ya daina binciken ne, lokacinda ya gaya mashi cewa, yana fata Comey zai yi watsi da binciken Flynn.

Trump yace bayanan Comey akan tattaunawar da suke yi a kan Flynn ba daidai bane.

Facebook Forum

Bidiyo

Mijin Aljana A Kano: Shin Dama Aljanu Na Da ATM’ Na Kudi?
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG