Accessibility links

Wasu 'Yan Bidiga Sun Gamu Da Fushin 'Yan Jihar Adamawa


Wani dan Sanda yana sunturi a harabar hukumar 'yan sanda dake Kano.

Wasu 'yan fashi da makami da suka farwa wani kantin zamani da ake kira "Super Market" dake unguwar Nasarawa cikin garin Jimeta-Yola, sun gamu da fushin mazauna unguwar.

WASHINGTON, D.C - Al’umman garin Jimeta,fadar jihar Adamawa sun yi kukan kura a jiya Juma'a, inda suka tarwatsa wasu mahara da ake kyautata zaton cewa yan fashi da makami ne.

Wani mazaunin unguwar ya bayanna irin halin da suka shiga bayan da aka fara harbe-harben. Yace "An firgita mu, an wayi gari mun ji ana harbe-harbe".

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, DSP Muhammed Ibrahim yace an kashe 'yan bindiga su shida a musayar wutan, sannan jami'an tsaro sun kwace bindiga guda daya samfurin AK 47 da harsashai 101.

Shugabannin al-ummar sun dauki alwashin daukar mataki ga duk wani mai kokarin tayar musu da hankula. Alhaji Hamma Adma Alijo, wanda shine kantomar raya kasa na wannan guduma yace "Zaman lafiya yafi komai, kuma zamu bada fifiko akan tabbatar da tsaro."

Harbe-harben ya faru ne kasa da sa'o'i hudu bayan wani hari a garin Malabu dake kan iyaka, a wannan jiha dake Najeriya.

XS
SM
MD
LG