Kwamitin janar Magoro na ci gaba da neman tantance gaskiyar al'amarin da ya faru a Baga
WASHINGTON, DC —
Janar Mahamadu Magoro shugaban kwamitin harakokin tsaro a majalisar dattawan Najeriya, kuma wanda aka dorawa nauyin jagorantar binciken abubuwan da suka faru a Baga ya kai ziyara jahar Borno tare da tawagar sa. Ma'aikaciyar Sashen Hausa Jummai Ali wadda ke jahar Borno yanzu haka ta tattauna da Janar Mahamadu Magoro da kuma Kanal Saghir Musa kakakin rundunar musamman ta tabbatar da tsaro a jahar Borno, JTF. Janar Magoro ne ya fara yiwa Jummai Ali karin haske a kan ayyukan da aka dorawa kwamitin su na binciken abun da ya faru a Baga.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 27, 2023
Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Kauce Hanya
-
Janairu 27, 2023
Za Mu Daukaka Kara – Adeleke
-
Janairu 27, 2023
Osun: Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Soke Nasarar Adeleke