Shin Kuwa Da Gwamnati A Kasar Najeriya?

Tabarbarewar matsalar tsaro a Najeriya ta sa wasu masanan kasar na tambaya ko da gwamnati a kasar
WASHINGTON, DC —
wakilin Sashen Hausa Ladan Ibrahim Ayawa ya maida hankali akan tabarbarewar tsaro a Najeriya kuma ya hada ma na raton cewa tabbatar da tsaron al'umma na daga cikin hakkokin da suka rataya a wuyan gwamnati a duka duniya, amma a Najeriya ba haka abun yake ba in ji masu lura da al'amuran yau da kullum. Yau ka ji an kashe wannan jami'i, gobe ka ji an kashe mataimakin wannan jami'i, wanda hakan ya sa wasu 'yan kasar yin tambayar cewa anya kuwa da gwamnati a Najeriya? Masu lura da al'amuran na yau da kullum sun ce an rasa inda Najeriya ta sa gaba, suka ce abubuwan da suka wakana kwanan nan a Baga da Bama da Bayelsa da kuma Nasarawa, ko a yakin basasa ba a ganin irin haka, ga kuma wasu 'yan kasar shafaffu da mai, su na ta furta kalaman da ka iya hargitsa kasa, amma ko uffan gwamnati ba ta cewa da su. Dr. Saddiq Abubakar na daga cikin irin wadannan masana da ke lura da abubuwan da ke faruwa a Najeriya.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 29, 2023
CBN Ya Kara Kwana 10 Kan Wa’adin Daina Karbar Tsofaffin Kudi
-
Janairu 27, 2023
Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Kauce Hanya
-
Janairu 27, 2023
Za Mu Daukaka Kara – Adeleke