Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Kasar Cuba Na Zuwa Don Ban Kwana Da Shugabansu


Ana sa ran dubun dubatan mutane zasu yi cincirindo a shahararren filin nan na Revolutionary Square, ko dandalin Juyin Juya Hali na birnin Havana a yau litinin, yayin da kasar Cuba ta fara zaman makokin sati daya na yin ban kwana da marigayi Fidel Castro, mutumin da wasu ke matukar kauna, wasu kuma suke yin gaba da shi.

Wani mutum mai suna Jose Luis Herrera yace “ Wanene mutuwar wannan mutum bata shafa ba, Mutumin da yayi mana komai a rayuwa”.
Berta Soler kuwa Shugabar Yan adawa da Castro ta kungiyar Ladies In The White tace, “ Bama murnar mutuwar Dan Adam, Muna murnar mutuwar Mai mulkin kama karyane.”
Castro dan Shekaru 90 ya rasu ranar Jumu’a, bayan tsawon rashin lafiya. Har yanzu dai ba’a bayyana dalilin da ya jawo rasuwar tasaba.
An sauke tutoci a ko’ina a tsibirin na Cuba.
A ranar Laraba mai zuwa za’a dauki tokar Castro zuwa gabashin kasar inda za’a kwashe kwanaki uku a hanyar da Dan rajin yabi a lokacin da yabi Mayakan Canjin a lokacin da suka kusanci Havana daga Tsaunukan Sierra Maestra kafin ya kabi mulki a Watan Janairu na shekarar 1959.
Za’a Binne shi a ranar 4 ga watan Disamba a Kudu maso Gabasshin Birnin Santiago De Cuba a Makabartar Santa Lfigenia.
Jiya Lahadi a Miami Yan Kungiyar Ladies In The White suka hadu da sauran kungiyoyin da ke adawa domin yin Tattaki akan nuna goyon bayan Dimokradiyya a Cuba a ranar Laraba.
An kafa kungiyar Ladies in The white a shekarar 2003 don tallafawa Mazajen da aka daure akan adawar siyasa a kasar da ake da Jam’iyya daya. Kungiyar na shirya tattaki a duk sati a Havana tsahon shekaru 13.
A wurin da ake kira Little Havana a Miami dake Florida Yan Cuban dake America sun fito tituna suna raye raye da murnar mutuwar Castro.

XS
SM
MD
LG