Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Senegal Sun Dunguma Zuwa Rnufunan Zabe A Yau Lahadi


Shugaban kasar Senegal Macky Sall yana kada kuri'a

A yau Lahadi ne masu kada kuri’a a kasar Senegal zasu yi zabe domin zabo sabon shugaban kasa.

Shugaba Macky Sally a fada a wurin wani taron gangami, cewa ko shakka babu zai lashe zaben ba tare da an je zagaye na biyu ba.

Amma kungiyoyin kare hakkin bil adama sun caccaki Sall saboda haramtawa wani babban dan adawarsa shiga takarar ta yau Lahadi.

Dole ne dai dan takara ya samu sama da kashi hamsin cikin dari na kuru’un kafin yayi nasarar zama shugaban kasar Senegal. Idan babu dan takarar da ya samu rinjaye, manyan ‘yan takara biyu zasu fafata a zagaye na biyu a cikin watan Maris..

Anasa ran samun sakamakon zaben kafin ranar Juma’a.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG