Shugabannin harkokin kasuwancin kasar Birtaniya suna kara gabatar da bukatocinsu da suka shafi ficewar kasar daga Kungiyar Tarayyar Turai-KTT, yayinda suke kokarin amfani da sakamakon zaben da aka gudanar makon da ya gabata, da ya raunana jam’iyar Conservative ta Theresa May, da ta gaza samun rinjaye kai tsaye a majalisa.
Suna kamun kafar gwamnati ta nemi dangantaka ta kut da kut da KTT fiye da yadda May tayi niyar yi da farko, wadda take kokarin ci gaba da mulki, a kalla na karamin lokaci, yayinda take fuskantar fushin jam’iyarta bisa sakamakon zaben da aka gudanar makon jiya.
Yana da wuya a iya fadin irin tasirin da rashin tabbas a harkokin siyasaryake da shi a kan shugabannin cibiyoyin kasuwanci, da kuma irin illar da zai yi ga tattalin arzikin Birtaniya idan ba a dauki matakin gaggawa ba, inji Martin, Kimanin kashi saba’in da biyu cikin dari na membobin kungiyar dake tattaunawa a madadin cibiyoyin kasuwanci, sunce ya kamata batun sake cimma wata yarjejeniyar cinikayya ta kasance abu mafi muhimmanci ga sabuwar gwamnati.
Shugabannin harkokin kasuwanci, dake daukar sakamakon zaben a matsayin tsayayya da shirin May na ficewa daga KTT, suna kira ga Firai Ministan ta tabbatar da ‘yancin zama kasar ga ‘yan kasashen turai miliyan uku da suke zaune a Birtaniya a halin yanzu, bisa hujjar cewa, suna da tasiri ga tattalin arzikin kasar.
Suna kuma so su iya harkokin kasuwanci a kasuwar daya ba tare da biyan kudin fito ba.
Facebook Forum