Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasuwa A Jihar Kano Sun Yi Gangamin Neman Daidaito


A jiya ne Kungiyoyin ‘yan kasuwa dana masu kanana da matsakaitan masana’antu a jihar Kano suka gudanar da wani maci a domin nuna goyon bayan su ga wani kudirin doka da aka yiwa lakabi da NATITIONAL COMPETITION BILL.

Kudirin dai na kokarin kyautata gasa da neman baiwa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da masu aikin kere-kere cikakkiyar damar gogayya da manyan kamfanoni da masana’antu ta fuskar kayayyakin da suke sarrafawa ko kuma ayyukan da suke gudanarwa a cikin kasa.

Alhaji Rabi’u M. Kura shine sakataren gamayyar kungiyoyin ‘yan kasuwa reshen jihar Kano kuma ya yi kira ga hukumar da alhakin ya rataya a wuyanta data taimaka wajan tabbatar da aiwatar da wannan kudiri nasu domin a cewar sa sun gaji a abin da ya kira kashin dankali, wato manta suna tattake kanana.

Hussaina Ahmad Umar, mataimakiyar masu kananan masana’antu ta kasa kuma mai zama da kuma masana’antar mangyada a jihar ta Kano ta ce sun halarci gangaminne domin nuna goyon bayansu a kan wanna kudiri.

Ta kara da cewa masu kananan masa’antu na samun tsaiko saboda manyan kamfanoni sun yi kaka gida, sun hana su sukunin gudanar da kasuwancin su da kuma samun ci gaba.

Matchin enable kungaiya ce dake karkashin hukumar kula da kasashe masu tasowa ta Burtaniya ta shirya wannan gangamin, da aka yi tattaki daga cibiyar ‘yan jarida ta jihar Kano zuwa harabar ma’aikatar yada labarum jihar.

Daga Kano ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Shiga Kai Tsaye

AFCON 2021, Kelechi Iheanacho

"Ku doke daya daga cikin shahararrun koci a duniya", Kelechi Iheanacho, Najeriya bayan sun doke Masar
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:11 0:00
Karin bayani akan Wasanni

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG