Wasu ‘yan kunar bakin wake na zauna kusa da wasu dimbin fasinjojin da aka yi garkuwa da su bayan da mayakan suka yi awon gaba da wani jirgin kasa a kudu maso yammacin Pakistan, lamarin da ya rikita ayyukan ceto, kamar yadda majiyoyin tsaro suka bayyana a ranar Laraba.
Kimanin 'yan aware 50 ne suka tarwatsa hanyar jirgin kasan tare da harba rokoki a tashar Jaffar Express a ranar Talata, wanda ke dauke da mutane sama da 400, in ji wani jami'in tsaro.
Daruruwan sojoji da tawagogi a cikin jirage masu saukar ungulu sun gudanar da aikin ceton mutanen da aka yi garkuwa da su a yankin tsaunuka mai nisa da aka tsayar da jirgin kasan. Gwamnati ta ce kawo yanzu dai ta ceto fasinjoji 155.
Babu dai wani bayani a hukumance kan adadin mutanen da suka rage a hannun mayakan. Dakarun Kwato 'Yancin Baloch, wata kungiyar 'yan kabilar Baloch mai gwagwarmaya da makami, wacce ta dauki alhakin kai harin, ta ce a ranar Talata ta yi garkuwa da mutane 214.
Dandalin Mu Tattauna