Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Kwadago Sun Fara Siyasantar Da Ayyukan Su - ‘Yan Najeriya


Zanga-zangar NLC
Zanga-zangar NLC

‘Yan Najeriya sun fara nuna rashin jin dadinsu da salon kungiyoyi da suka ce talaka suke kara kuntatawa, kasa da sa’o’i 24 da fara yajin aikin gamagari da kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC suka fara.

A yau Talata ne ‘yan Najeriya suka wayi gari da yajin aikin gamagari da kungiyoyin kwadago na kasar wato NLC da TUC suka tsunduma a ciki duk da umarnin dakatar da yin yajin da kotun ma’aikatan kasar karkashin jagorancin, Mai Shari’a Benedict Backwash Kanyip, ta yi a makon jiya.

Daga misalin karfe 10 safiyar yau ne dai ‘yan Najeriya a manyan birane musamman babban birnin tarayyar kasar Abuja , suka fara ganin sakamakon yajin aikin yayinda wadanda ke fitowa harkokinsu na yau da kullum suka fuskanci karancin motocin zirga-zirga, katsewar wutan lantarki, rufe ofisoshin ma’aikatan gwamnati da dai sauransu.

Tuni dai wasu mazauna birnin Abuja da wasu sassan kasar daban-daban kama daga Kaduna, Nasarawa, Borno da dai sauransu suka fara nuna rashin jin dadin su da salon da kungiyoyin kwadago ke dauka na yajin aiki ba tare da la’akari da matsin da suke sanya talakawa wadanda ya kamata suna karewa a ciki ba, inda wasu ke cewa an fara siyasantar da harkokin kungiyar.

Zanga-zangar NLC
Zanga-zangar NLC

A hirar shi da Muryar Amurka, Da sakataren tsare-tsaren kungiyar NLC, kwamared Nasir Kabir ya ce kungiyar na nan daram a kan matakin da ta dauka kuma tana ci gaba da hada kan mambobinta. Bisa ga cewarsa, yajin aiki na tafiya yadda aka saba, ya kuma bayyana cewa, kungiyar zata fitar da sanarwa a kan matakin ta na gaba nan bada jimawa ba.

Rahotannin sun yi nuni da cewa gwamnatin kasar ta bakin Ministan kwadago da ayyukan yi, Simon Lalong, ta kira taron gaggawa da shugabannin kungiyoyin kwadago yayin da aka fara yajin aikin a fadin kasar, sai dai ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, kungiyoyin basu ce uffan a game da gayyatar da aka yi musu ba.

Wata zanga-zangar lumana ta NLC a Najeriya
Wata zanga-zangar lumana ta NLC a Najeriya

Ita ma kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ta shiga yajin aikin sai baba-ta-gani da kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da TUC suka shelanta.

Yajin aikin na kungiyoyin NLC da TUC dai ba ya rasa nasaba da sa-in-sa da ya wakana tsakanin shugaban NLC Joe Ajaero da gwamnatin jihar Imo wanda tuni masu sharhi a kan al’amurran yau da kullum suka ce bai dace a tsayar da ayyukan yau da kullum na miliyoyin yan Najeriya cir a bisa rikici tsakanin jiha da wani mutum ba.

Saurari Cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

NLC na kan bakar ta na yajin aiki - Nasir Kabir.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG