Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Zaben Liberia na ci Gaba da Kirga Kuru'un Zaben Raba Gardama


Zaben Kasar Liberia
Zaben Kasar Liberia

Al’ummar kasar Liberia na ci gaba da jiran sunan mutumen da zai zama sabon shugaban kasarsu a daidai lokacinda jami’an Hukumar zabe ke ci gaba da kirga kuri’un da aka jefa a zaben baya-bayan nan na raba gardama.

Tsohon zakaran kwallon kafa George Weah da mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai ne suka fafata wurin ganin dayansu ya gaji shugaba Ellen Johnson Sirleaf, wacce ta kare wa’adinta na biyu da kundin tsarin mulkin Liberia ya yarje mata.

Duk da cewa Hukumar Zabe ta Liberia ta fada a shafin Facebook cewa watakila a yau Alhamis zata bayyana sakamakon zaben, tuni George Weah ya bayyana imanin cewa shine zai lashe shi.

masu lura da yadda aka gudanarda zaben, wadanda suka hada da tsohon shugaban Nigeria, Goodluck Jonathan sun zagaya rumfunan zaben daban-daban, kuma dukkan alamu sun nuna cewa an gudanar da shi ba tareda fuskantar matsaloli da yawa ba.

Masu sukar lamirin Baokai dan shekaru 73 da haifuwa, sunce bai yiwa kasa komai ba a matsayinsa na mataimakin shugaba Sirleaf. Su kuma masu sukar Weah mai shekaru 51 a duniya sunce bashi da cikakkiyar kwarewa a harkar siyasa ko gudanar da mulki.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG