Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Majalisar Dokokin Najeriya Da Suka Mutu A Majalisa Ta 9


Maitala (dama) Okoji (sama hagu) Osinowo (kasa hagu) (Hoto: Instagram/Twitter)
Maitala (dama) Okoji (sama hagu) Osinowo (kasa hagu) (Hoto: Instagram/Twitter)

Akalla 'yan majalisar dokokin Najeriya shida ne suka rasu a majalisa ta 9 (mai zauruka biyu) wacce aka rantsar da mambobinta a ranar 11 ga watan Yunin 2019.

Dan majalisa na baya-bayan nan da ya rasu shi ne, Alhaji Haruna Maitala​ da ke wakiltar mazabar Bassa/Jos North (Plateau) a majalisar wakilan kasar mai mambobi 360.

Ya rasu ne a ranar Juma’a a hatsarin mota yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Jos daga Abuja, don halartar daurin auren dansa da aka shirya za a yi a ranar Asabar kamar rahotanni suka nuna.

Maitala wanda dan majalisa ne da ke wakiltar mazabarsa a karon farko, ya rasu tare da dansa, da wasu hadimansa biyu.

Karin bayani akan: ‘Yan Majalisar Dokokin Najeriya, Rose Okoji Oko, Alhaji Haruna Maitala​, Nigeria, da Najeriya.

Shi ne ya maye gurbin Suleiman Kwande, wanda ya kayar a zaben 2019.

Tuni an yi jana’izarsa a Jos a ranar Asabar.

Rasuwar Maitala na zuwa ne, kusan wata guda bayan rashin dan majalisar wakilai Yuguda Hassan Kila da aka yi, wanda ya wakilci mazabar Gwaram daga jihar Jigawa. Shekarasa 65.

Benjamin Uwajumogu (Hoto: Freshnewsng/ Instagram)
Benjamin Uwajumogu (Hoto: Freshnewsng/ Instagram)

Sauran ‘Yan Majalisar Dokokin Najeriya da suka rasu a wannan majalisa ta tara sun hada da:

- Senator Adebayo Osinowo wanda ake wa inkiya da “Pepperito” (mazabar Gabashin jihar Lagos -Lagos East,) ya rasu ne a ranar 15 ga watan Yunin 2020. Shekararsa 64.

- Senator Benjamin Uwajumogu (mazabar Arewacin jihar Imo – Imo North,) ya rasu a ranar 18 ga watan shekarar 2019. Shekararsa 51.

Ignatius Longjang
Ignatius Longjang

- Senator Ignatius Longjang (mazabar Kudancin Plateau – Plateau South) ya rasu a ranar 10 ga watan Fabrairu 2020 bayan fama da rashin lafiya. Shekararsa 75.

- Senator Rose Okoji Oko (mazabar arewacin jihar Cross River – Cross River North) ta rasu a ranar 23 ga watan Maris 2020 bayan fama da rashin lafiya. Shekararta 63.

XS
SM
MD
LG