Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dokokin Rasha Sun Ziyarci Shugaba al-Assad a Syria


Shugaban Rasha Putin da Shugaba al-Assad na Syria
Shugaban Rasha Putin da Shugaba al-Assad na Syria

'Yan majalisar dokokin kasar Rasha sun kai ziyara Syria inda suka gana da shugaban kasar kafin su gayawa manma labarai cewa shugaban yace ashirye yake ya gudanar da zaben shugaban kasa da ana majalisa

A Syria shugaban kasar Bashar al-Assad ya sake nanata kudurinsa na maida hankali wajen kawarda barazanar 'yan ta'adda a kasarsa, shugaban wanda yayi magana jiya lahadi, yace hakan ne zai kai ga samar da maslahar da 'yan kasar suke nema ga rikicin siyasar data addabe su, fiyeda shekaru hudu da rabi yanzu.

Shugaba Assad ya bayyana haka ne lokacinda wata tawagar wakilan majalisar dokokin Rasha suka gana da shi a Damascuss. Wani dan majaisar dokokin Rasha yace Assad a shirye yake ya ya gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisa muddin shine bukatar 'yan kasar.

Ma'aiatar harkokin wajen Rasha tace sakataren harkokin wajen Amurka John kerry a tattaunawar da yayi d a takwaran aikinsa na Rasha Sergei Lavrov ta wayar tarho sunyi magana kan "damar" kulla yarjejeniyar sulhu a Syria tareda goyon bayan hukumomin kasa da kasa, da zai kunshi hukumomin kasar da kuma 'yan hamayya wadanda suke kishin kasa.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG