Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Majalisar Koriya Ta Kudu Zasu Zabi Fara Ministan Da Suke So


Shugabar Kasar Koriya ta Kudu

Shugabar kasar Koriya ta Kudu, Park geun-hye, tace zata bar yan majalisar kasar su zabi sabon Firaminista , saboda tana kokarin tsallake rikice rikicen siyasar cikin gida da take fuskanta.

Shugaban kasar ta bayyana haka ne a jiya Talata bayan zaman tattaunawa da tayi da Chung Sye-kyun, kakakin babbar majalisar da yan adawa suke rike da ita. Sannan bayaga barin zaben sabon Firaminista , Park ta yarda da shi zai ja ragamar jami’an gwamnatin.

A kwanan nan ne Shugaban kasar ta tsayar da Kim Byong-Joon Babban matsayin , amma Yan adawa dake cikin gwamnatin suka ki amince da zama da sauraron Mukamin.

XS
SM
MD
LG