Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Tarayyar Amurka Sun Nemi a Kakabawa Rasha Takunkumi


'Yan Majalisar Tarayyar Amurka da wasu tsoffin jami'an diflomasiyya, jiya Alhamis sun bukaci da a kakaba ma kasar Rasha takunkumi mai tsanani, to amma sun jaddada muhimmancin bullo da matakan da za su ja hankalin Rasha ba tare da yin illa ga Amurka ko kawayenta na Turai ba.

"Babu tantama ko kadan, cewa dole ne Shugaban Rasha Vladimir Putin ya dandana kudarsa saboda abin da ya aikata, kuma Amurka za ta iya kakaba takunkumin da zai janyo matukar asara ga Rasha," Ciyaman din sashin banki a Majalisar Dattawa, dan Republican daga Idaho Mike Crapo, ya fadi a zaman da aka yi cewa, "Mu na bukatar Rasha ta gaggauta yin sahihin canji a halayyanta," a cewar wani babban mamban kwamitin, dan jam'iyyar Dimokarat, Sherrod Brown mai wakiltar Ohio, wanda ya kara da cewa, "Har yanzu ba mu fara ganin wani canji ba."

A yayin zaman na jiya Alhamis, tsohon Jakadan Amurka a Rasha, Michael McFaul, ya yi kira ga 'yan Majalisar Tarayyar Amurka da su dada matsa lamba ma Rasha.

"Dole hukunci ya biyo bayan duk wani mummunan laifi. Ina kira kare ku, da ku kara azama."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG