Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majlisun Kasar Turkiyya Sun Yi Gangamin Nuna Goyon Bayan Mulkin Demokaradiyya


‘Yan majalisun Turkiyya daga jam’iyyun kasar biyu sun yi gangami tare don nuna goyon bayansu ga dimokaradiyya da kuma yin Allah wadai da kokarin juyin mulkin da aka yi na ranar 15 ga wannan watan da muke ciki.

Dandalin Taksim dake birnin Istanbul, wanda kuma babbar jam’iyyar adawa ta Republican Peoples Party ta hada, Inda suka hadu da sauran jam’iyun siyasar kasar, ciki harda jam’iyyar shugaban kasa Tayyip Erdogan ta Islamic Justice wadda ta mulki kasar tun shekara ta 2002.

Wani al'amarin kuma na bayyana hadin kan 'kasa ya fito daga Shugaban Rundunar Sojojin Sama na Turkiyya, wadda ta fitar da wata takarda mai ban mamaki, da ke jaddada goyon baya ga Hafsan Hafsoshin Soji, Hulusi Akar.

Wasu daga cikin rundunar sojan sama na daga cikin sojojin da suka yi kokarin juyin mulkin, lokacin da aka yi garkuwa da Akar.

Shugaban kasa Erdogan, wanda ya kauce ma kamu da yiwuwar kisa, ya ayyana dokar ta baci a kasar, wadda zata ba shi damar aiwatar da doka ba tare da amincewar ‘yan majalisa ba, a kokarin neman duk wadanda ke da hannu a juyin mulkin, wanda akalla mutane 246 suka rasa rayukansu ciki, wasu sama da 2000 suka raunata.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG