Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tim Kaine Ya Yi Jawabin Amincewa Da Tayin Zama Mataimakin Hillary


Tim Kaine a Lokacin Jawabinsa Na Amincewa Da Tayin Zama Abokin Takarar Hillary Clinton a Matsayin Mataimakin Shugaban Kasa, July 23, 2016.

Sanata Tim Kaine da ‘yar takarar neman shugabancin Amurka da ake sa ran Jam’iyyarta ta Republican ita zata tsayar wato Hillary Clinton ta bayyana a jiya Juma’a a matsayin mataimakinta idan ta zama shugabar kasa, ya yi jawabin amincewa da wannan tayi.

Inda ya mika jawabinsa ga dimbin jama’ar da suka taru a birnin Miami na jihar Florida. Tim yayi bayani mai karfi da shiga jikin masu sauraronsa, a lokacin da yake magana yana hadawa da yaren Sifaniyanci kai kace yarensa ne na haihuwa, alhali koya yayi.

Kaine dai tsohon dan jam’iyyar Democrat ne wanda ya bayyana kansa a matsayin gundura, to amma yana da sassaucin ra’ayi, kuma ana kallonsa a matsayin wanda ke da kwarewar da zai iya canza ra’ayin masu zabe su guji Trump su zabi Hillary.

Sanata Tim yana da kima sosai a idon jama’a, sannan ya jaddada cewa bai taba faduwa zabe ba tun da ya fara siyasa, kama tun daga zamansa Magajin Gari Richmond har zuwa zamansa gwamnan jihar Virginia da kuma zamansa Sanata.

Hillary ta kara da cewa, Tim yana cikin Sanatocin da na sani da suke da matukar kima a idanun jama’ar Amurka. Kamar yadda ta fadawa gidan talbijin na CBS.

Tim haifaffen jihar Minnesota ne, ya kuma yi karatun aikin Lauya a Jami’ar Harvard, jami’ar da ita ta haifar da Lauya Barack Obama da a yanzu haka ya ke shugabancin Amurka.

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG