Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen G20 Sun Lashi Takobin Farfado Da Tattalin Arzikin Duniya


Ministoci Da Shugabannin Bankunan Gwamnatin Kasashen G20 Masu Karfin Tattalin Arziki a Taronsu Yau a Chengdu, China, July 24, 2016.
Ministoci Da Shugabannin Bankunan Gwamnatin Kasashen G20 Masu Karfin Tattalin Arziki a Taronsu Yau a Chengdu, China, July 24, 2016.

Ministocin hada-hadar kudaden kasashe 20 mafi karfin tattalin arziki a duniya, sun sha alwashi habaka tattalin arzikin duniya, wanda suka ce yana raurawa wajen farfadowa a duniya.

Wakilan kasashen sun fidda sanarwar haka ne a yau Lahadi daga birnin Chengdu dake kasar Sin, a lokacin da suka kammala taron nasu na kwana biyu.

Cikin abinda suka tattauna a taron har da matakin fitar Birtaniya daga kungiyar kasashen Turai. Wanda suka ce hakan zai taba tattalin arzikin duniya ta wata fuskar.

Duk da yake dai sun bayyana cewa, kashen da suke membobin G20 din sun yi tsayuwar dakan yadda zasu tari lamarin na tangadin tattalin arziki.

Sanarwar ta bayan taron G20 ta jaddada kira ga muhimmancin rage yawan samar da karafan kere-kere wanda hakan ke sa ambaliyar karafa a kasuwar duniya.

Musamman yadda China da kawayenta suke sayarwa duniya karafa cikin saukin farashi.

XS
SM
MD
LG