Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Matan Dapchi 101 Aka Mayar Cikin 110 - inji Lai Mohammed


'Daya daga cikin 'yan matan Dapchi da aka saki.
'Daya daga cikin 'yan matan Dapchi da aka saki.

Ministan watsa labaran Nijeriya ya ce yan ta’addar Boko Haram sun saki yan mata 101 cikin 110 da suka sace a Arewa maso gabashin Najeriya a garin Dapchi a watan da ya gabata.

Lai Mohammed ya gaya wa manema labarai a Abuja cewar yan matan hade da wani yaro guda ‘daya an ajesu ne a wurare daban daban a kan hanyar garin Dapchi.

A cewar ministan “Ina tabattar da cewa ya zuwa yanzu an sako ‘yan mata 101 da kuma yaro ‘daya namiji. Wannan labari ne da yake faruwa a yanzu. Kuma bisa ga dukkan alamu ba a wuri ‘daya aka ajiye su ba.”

Ofishin ministan na watsa labarai dai ya ce an saki yan matan ne da misalin karfe 3 na dare da taimakon “wasu kafofi da akayi amfani dasu da kuma taimakon wasu abokanen kasar ta Nijeriya.”

Ofishin shugaban kasar Nijeriya ya ce yan matan dai yanzu haka suna gida a Dapchi ana kuma kididdigar su. Sai dai kuma ofishin yace babu wani kudin fansa da aka biya kafin sakin nasu.

Mazauna garin na Dapchi sun bayyana cewa mayakan Boko Haram dinsun tuko yaran zuwa garin Dapchi a cikin motoci 9 suka aje su suka tafi.

Har yanzu dai ba’a san makomar sauran yaran da ba’a saki ba.

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG