Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Na Nuna Fusatarsu Da Dage Zabe


Shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa Attahiru Jega

Da yawa sun ce zai yi wuya wadanda suka tafi har zuwa wasu garuruwa don jefa kuri'a a zaben na 'yan majalisar dokokin tarayya su sake komawa ranar litinin

Al’umma a Najeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama’a a nahiyar Afirka, su na ci gaba da nuna fusata da kuma bacin ransu a bayan da hukumomi suka jinkirta zabubbukan ‘yan majalisar dokokin tarayya jiya asabar.

Jiya asabar din, shugaban hukumar zabe ta Najeriya, Farfesa Attahiru Jega, ya fito a telebijin yana dora laifin jinkirta zaben a kan kamfanin da aka bai wa kwangilar samar da takardun kuri’a da na zana sakamakon zabe, kayayyakin da yace kamfanin ya kasa kai su zuwa rumfunan zaben a kan lokaci.

Jega yace an karkata hancin jiragen da zasu yi jigilar kayan zaben zuwa Najeriya suka koma daukar kayan agajin jinkai zuwa kasar Japan, wadda ta fuskanci bala’i na girgizar kasa da ambaliyar ruwa a sanadin munanan igiyoyin ruwa da kuma yoyon masana’antar nukiliya.

Jega yayi alkawarin za a sake gudanar da wannan zabe ranar litinin.

Shugaba Goodluck Jonathan, wanda shi ma rumfar zaben da zai jefa kuri’arsa a ciki ba ta samun kayan zaben ba, ya roki ‘yan Najeriya da su nuna hakuri. Amma masu jefa kuri’a da dama sun nuna bacin rai da kuma fusata, su na masu fadin cewa mutane da yawa da suka yi tafiya mai nisa domin zuwa garuruwan da zasu jefa kuri’a ba zasu iya komawa ranar litinin ba.

A ranar jumma’a dai, watau ranar jajiberen zaben, Jega bai nuna alamun cewa akwai wata matsala ba, a maimakon haka ya fito ne yana fadin cewa wannan zabe na Afrilu zai ba ‘yan Najeriya damar nunawa duniya cewa sun iya zabe a bayan da aka fuskanci zub da jini da mummunan magudi a zaben 2007.

XS
SM
MD
LG