Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Labari Da Dumi-Duminsa: Zaben 2011 a Najeriya


A nan, jami'an zabe ne ke jiran isowar kayan aiki a wani wurin rarraba kayan dake Ibadan, Nigeria, ran Assabar, 2 ga watan Afrilun 2011.

Hukumar zaben Nigeria ta bada sanarwar jinkirin mako daya ga zabbukkan kasar. Zaben 'yanmajalisun dokoki da aka jinkirta, yanzu an shirya za'ayi shi ran Assabar, 9 ga watan Afrilu, shi kuma na shugaban kasa za'ayi shi ran 16 ga watan Afrilu, yayinda zaben gwamnoni kuma za'ayi shi ran Talata, 26 ga watan Afrilu. Wannan shine karo na biyu da ake jinkirta zaben. A can farko, ran 2 ga watan Afrilu ya kamata soma da zaben 'yanmajalisa, aka dage, akace sai ran Litinin, 4 ga watan na Afrilu, sai gashi yanzu kuma an sake dagewa ta biyu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG