Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Najeriya Sama Da Dubu Goma Sha Shida Aka Maido Gida Bara: Babandede


'Yan ci rani daga Kasar Libiya
'Yan ci rani daga Kasar Libiya

Shugaban hukumar shige da fice na Najeriya Alhaji Mohammed Babandede yace a bara an dawo da ‘yan Najeriya dubu goma sha shida da dari uku da tamanin da bakwai da suka makale a kasashen ketare ko suke zaune a kasashen ba da takardun izinin zama ba.

Mutanen, wadanda ke cikin mutanen, dubu biyar da dari tara da tamanin, an dawo dasu ne daga kasar Libiya, sannan aka dawo da wasu dubu uku da dari takwas da talatin da shidda daga kasar Saudiya, sai kuma dubu shidda da dari shidda da arba’in da uku da aka dawo da su daga Afrika ta Kudu da kasashen Turai.

Masu kula da lamura sun bukaci gwamnati tayi kyakkyawan nazarin tsarin shugabanci wanda zai iya taimakawa wajen sauya lamura.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Nasiru Adamu El-Hikaya ya aiko daga Abuja:

Rahoton Kan batun 'yan cirani-4:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:05 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG