Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan PDP Sun Koka da Zargin Fadi Daura


PDP logo

'Yan PDP Sun Koka Da Zargi Fadi Daura

'Yan PDP fiye da dubu daya daga yakin Michika na jihar Adamawa suka kai kokensu a hedkwatar jam'iyyar bangaren Bamanga Tukur.

'Yan jam'iyyar da suka fito daga Michika sun nuna bacin ransu sun ce sun gaji da shirin fadi daura da a keyi masu. Sun ce lamarin ba zai haifarwa jama'iyyar da mai ido ba. Alhaji Sabo Barta yana cikin wadanda suka yi jawabi. Ya ce abun da aka yi ya basu tsoro dalili ke nan suka zo domin a san na yi. Sun kawo kukansu a rubuce domin danniya da a keyi masu.

A wata sabuwa kuma sakataren watsa labarai na jam'iyyar ya rubuta takardar barin aiki da kuma barin jam'iyyar gaba daya. To saidai Jori Madaki shugaban PDP bangaren Bamanga Tukur ya ce tafiyar sakataren watsa labaran albarka ce garesu domin kasancewarsa cikinsu zata kawo masu illa.

Jam'iyyar ta yi barazanar kwace kujerarta daga gwamna Nyako domin sauya shekar da ya yi zuwa APC. Ya ce ba zasu bari ba sai an bayyana masu wanene ya ci zabe jam'iyya ce ko dan takara. Haka ma ba'a san matakin da jam'iyyar zata dauka ba kan shugabanin kananan hukumomi 21 da tuni suka koma APC.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG