Accessibility links

'Yan Sanda A Kinshasa Sun Tarwatsa Magoya Bayan Shugaban 'Yan Hamayya.

  • Aliyu Imam

Wasu matasa da ake zargin magoya bayan shugaban 'Yan hamayya ake tilastawa shiga motar 'Yansanda.

‘Yan Sanda a Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango sun harba hayaki mai sa hawaye kan magoya bayan shugaban ‘yan hamayya Etienne Tshisekedi, wadan da suka hallara domin bikin rantsuwar kama aikin mutumin da suke goyon baya, bayan ya “ayyana kansa” shugaban kasa.

‘Yan Sanda a Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango sun harba hayaki mai sa hawaye kan magoya bayan shugaban ‘yan hamayya Etienne Tshisekedi, wadan da suka hallara domin bikin rantsuwar kama aikin mutumin da suke goyon baya, bayan ya “ayyana kansa” shugaban kasa.

Mr. Tshisekedi ya dage shi ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi cikin watan jiya, daga nan yayi kira ga magoya bayansa su hallara a babban dandali dake Kinshasa babban birnin kasar, domin bikin ranstuwar kama aikin sa.

Gwamnatin kasar ta haramta taron, kuma ta ta baza dakaru da motoci masu sulke da ‘Yan sanda ta ko ina a babban birnin kasar, musamman a unuguwannin da galibi Tshisekedi yake da goyon baya.

Tunda farko, wani mai bada shawara ga Tshisekedi ya gayawa Sashen Turanci na Muriyar Amurka cewa, za a yi bikin duk da barazanar da gwamnati tayi cewa zata kama madugun ‘yan hamayyan.

Hukumar zaben kasar ta ayyana shugaban kasar na yanzu Joseph kabila, a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da aka yi cikin watan jiya, amma Mr. Tshisekedi wadda yazo na biyu a zaben, yayi watsi da sakamakon da aka bayar, san nan ya ayyana kansa shugaban kasa.

Mai bada shawara ga madugun ‘yan hamayyan, Valentin Mubake yace Mr. Kabila ya lashe zaben ne kawai sabo da “tsagwaran magudi”, ya kuma yi watsi da ikirarin cewa Mr. Tshisekedi zai iya tada zaune tsaye a kasar.

XS
SM
MD
LG