Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Na Neman Mutumin Da Ya Kashe Mutane Hudu A Jihar Tennessee


Gidan cin abincin da Travis Reinking ya kashe mutane hudu

Travis Reinking wanda FBI ta taba kamawa domin shiga inda bai makata ba ana nemansa da zargin kashe mutane hudu tare da jikata wasu a wani wurin cin abinci kusa da Nashville a jihar Tennessee dake nan Amurka

'Yansanda a jahar Tennessee a nan Amurka, sun kafa tarko da nufin kama wani mutum mai suna Travis Reinking. Ana zargin Travis, dan shekaru 29 da haifuwa, da laifin kashe mutane hudu ya kuma jikkata wasu masu yawa a birnin Nashville, a tsakar daren Asabar da bindiga.

Wani ma'abucin gidan cin abincin, ya kwace bindigar daga hanun Travis ya wurgarda ita bayan kanta, sai a lokacin ne Travis, ya tube rigar sanyi dake jikinsa ya tsere tsirara daga inda ya kai harin.

Jami'an tsaro na musamman masu bada kariya ga shugaban Amurka da wasu manya, sun ce sun kama Travis cikin watan Yulin bara, saboda ya shiga wani wuri da ba'a shiga ba tareda izini ba, a kusada fadar shugaba ta White House.

‘Yan sandan Nashville sun ce hukumar FBI ta tantance cewa bai kamata a bar shi ya malaki makamai ba, a saboda haka aka baiwa mahaifinsa makamin da aka kwace a hanun dan, wanda ake zargin cewa daga baya mahaifin ya juya ya baiwa dan nasa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG