Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Na Neman Rahama Sadau


Rahama Sadau (Hoto: Twitter, @Rahama_sadau)
Rahama Sadau (Hoto: Twitter, @Rahama_sadau)

Bayan kwanaki da aka kwashe jama'a na tsokaci dangane da hotunan da jarumar Rahama Sadau ta wallafa wadanda suka bakanta ran al'umar Musulmi, jami'an tsaro na neman jarumar ta fim din "Mati A Zazzau."

Kafofin yada labarai a Najeriya, sun ruwaito cewa ‘yan sanda a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin kasar, sun gayyaci fitacciyar jaruma Rahama Sadau, bayan da wasu hotuna da ta wallafa a shafukan sada zumunta suka haifar da batanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

A makon da ya gabata Rahama ta wallafa wasu hotuna da suka nuna tsiraici wadanda suka janyo muhawarar da ta kai ga wani ya shiga sashin yin tsokaci ya rubuta kalaman batanci ga Annabi.

Lamarin ya janyo kakkausar suka har daga abokanan sana’arta, malamai da kuma jama’ar gari.

Jaruman da suka yi tir da hakan sun hada da Adam A. Zango, Sheikh Isa Alolo, Hafsat Shehu, Ali Nuhu, Ahmed Lawal, Ibrahim Sharukhan da sauransu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, Muhammad Jalige wanda Muryar Amurka ta tuntuba ya ce yana hutu, inda ya kara da cewa akwai wadanda suka hankalinsa kan lamarin zai kuma bincika ya name mu.

Mujallar Fim da ke wallafa labarai kan harkokin fina-finan Hausa a Najeriya ta ruwaito cewa, "Sufeton na 'yan sandan Nijeriya, Mohammed Adamu, ya ba Kwamishinan 'yan sanda na Jihar Kaduna umarnin ya binciki Rahama Sadau.”

Rahotanni sun yi nuni da cewa, jarumar tana birnin Abuja ne a lokacin da jami’an tsaro suka yi yunkurin kamata, amma aka ba da umurnin ta kai kanta ofishin ‘yan sanda da ke Kaduna a cewar rahotanni.

Gayyartar da aka yi wa jarumar, ta biyo bayan korafi da wani Alhaji Lawal Mohammed Gausau ya aikawa Babban Sufeton ‘yan sanda Najeriya, kan barazanar da ke tattare da barin lamarin ba tare da an yi bincike ba, wanda hakan a cewarsa, ka iya haifar da rikici a tsakanin al’uma kamar yadda rahotanni suka nuna.

Wannan lamari dai ya sa kungiyar masu hada fina-finai ta MOPPAN reshen arewacin Najeriya ta sanar da dakatar da jarumar wacce 'yar asalin jihar Kaduna ce.

Jim kadan dai bayan barkewar ce-ce-ku-cen, Rahama ta fito ta ba da hakuri tana mai nesanta kanta da kalaman batancin.

“Ni Musulma ce, iyayena Musulmai ne, dangi na gaba daya Musulmai ne, ba zan taba yin wani abu da zai taba Musulunci ko kuma mazon Allah S.A.W ba.” Rahama ta ce a wani faifan bidiyo da ta wallafa mai tsawon kusan minti uku.

Ta kara da cewa, “kaddara ce ta fada akan hotona.”

A shekarar 2016 kungiyar ta MOPPAN ta taba dakatar da ita, bayan da ta fito a wani bidiyon mawaki Classique inda aka ga suna rungumar juna.

Daga baya an dawo da ita cikin harkar finan-finan, duk da cewa akwai rahotanni da ke nuna an samu rarrabuwar kawuna a tsakanin shugaban kungiyar ta MOPPAN kan matakin janye dakatarwar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG