Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan sanda Sun Ce Mutane 18 Ne Suka Mutu a Harin Zamfara


‘Yan sanda suna daukan samfuri a inda aka kai harin bom da mota a Nyanya.

Wani hari da wasu mutane dauke da makamai suka kai a kan kauyen Birani, ya yi sanadin mutuwar mutum 18 a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya kamar yadda 'yan sanda suka tabbatar.

‘Yan sanda a Najeriya sun ce, wasu ‘yan bindiga sun harbe har lahira wasu mutane 18 a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar.

Kakakin ‘yan sanda jihar ta Zamfara, Muhammad Shehu, ya ce, ‘yan bindigar dauke da manyan makamai, sun yi wa wasu mazauna kauyen Birani kwantan-bauna a lokacin harin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya tabbatar.

Ya kara da cewa, ‘yan bindigar, wani gungun masu aikata manyan laifuka ne wadanda suka shahara wajen wajen satan shanu.

Ko da yake wasu kafofin yada labarai a Najeriyar, sun ruwaito cewa mutanen da ‘yan bindigar suka kashe sun kai 40.

Wannan hari, shi ne na baya-bayan nan a jerin hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa a kauyukan da ke arewa maso yammacin Najeriya, a yayin da sukan je satan shanu.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International, ta ce dubban mutane sun fice daga muhallansu kana an kashe mutum 168 daga farkon wannan shekara, sanadiyar rikicin manoma da makiyaya a jihohi biyar da ke Najeriyar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG