Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Na Binciken Mutuwar Dalibi Sylvester Oromoni Na Kwalejin Dowen


'Yan Sanda A Jihar Zamfara

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta sanar da cewa ta fara gudanar da bincike kan mutuwar marigayi Sylvester Oromoni, wani dalibin kwalejin Dowen mai shekaru 11 da ake zargin wasu dalibai suka ci zarafinsa har lahira a unguwar Lekki na jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Hakeem Olusegun Odumosu ya bayyana cewa an umurci sashin kisan kai na sashen binciken manyan laifuka da leken asiri na jihar legas wato SCID dake Panti, da ya karbe shari’ar daga sashin Maroko kamar yadda gidan talabijan na Channels ta bayyana.

Kwamishina Odumosu ya kara da cewa rundunar na hada kai da rundunar ‘yan sandan jihar Delta wajen gudanar da bincike domin bankado sirrin da ke tattare da mutuwar karamin yaro Sylvester Oromoni wanda ake zargin daliban ajin karshe na makarantar sakandare suka yi ajalinsa ta hangar lakada masa duka, da kuma ba shi wani sindarin chemical da ba’a iya tantancewa ba.

A game da ko ‘yan sanda za su yi amfani da sakamakon binciken lafiya da rahoton likita da iyayen marigayi Sylvesta suka yi, Odumosu ya ce za'a yi cikakken gwajin lafiya kuma za'a yi bincike don gano gaskiya a binciken yan sandan.

Marigayi dalibin wanda saura yan kwanaki ya cıka shekaru 12 a duniya ya mutu ne a ranar Talatar makon da ya gabata, bayan da ya sami raunuka da dama bayan zargin da ake yi cewa wasu manyan daliban makarantar sun gana masa azabar duka da cin zarafi mai tsananin gaske a yayin da yake dakin bacci da wasu dalibai.

A cikin wani faifan bidiyo da ya yi ta yawo a kafaffen sada zumunta, an ga Oromoni yana kukan jin tsananin zafi, hakoran sa sun yi jawur da jini, kafafunsa da ciki sun kumbura ya na cewa kar a taba shi.

Sakamakon jerin shaidun bidiyoyi da ke yawo a kafaffen sada zumunta, hukumar gudanarwar kwalejin Dowen ta fitar da wata sanarwa tana mai cewa za ta hada kai da hukumomi don zurfafa bincike kan lamarin.

Gwamnatin jihar Legas ta bakin ma’aikatar ilimi da ta kai ziyarar bincike tun farko a kwalejin a ranar Juma’a, ta sanar da cewa an rufe makarantar har sai yadda hali ya yi.

'Yan Najeriya da dama sun fara fitowa suna bayana cin zarrafi da suda fuskanta a makarantun kwana-kwanan sakandare har wasu na cewa ba zasu taba yafe wa manyan dalibai da suka ci mu su zarrafi ba sai sun je caban ubangiji.

Maryam Maigida mai zane-zanen zamani ta bayyana cewa akwai wata babbar daliba a makarantar kwana-kwana na FGC Bwari da ta ci zarrafinta saboda ba ta debo mata ruwa ba sakamakon ciwon kafa amma ta lakada mata duka ba kakkautawa.

Shima Kyaftin Ibrahim Shariff ya ce cin zarrafi da ya fuskanta a makarantar sakandare ya kusa jefa shi cikin mummunan yanayin kangarewa.

Ita ma Khadija Nasidi ta ce cin zarrafin da wata babbar daliba ta yi mata ya kusa makance ta.

Masu ruwa da tsaki dai sun fara yin kira ga hukumomin da nauyin kula da makarantu ya rataya a wuyansu su yiwa Allah su kula da tsarin ilimin Najeriya yadda ya kamata.

XS
SM
MD
LG