Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan sanda Sun Harbe ‘Yan bindigar IPOB Da Suka Kashe Gulak


'Yan sandan Najeriya yayin kaddamar da rundunar wanzar da zaman lafiya a jihar Enugu.(Twitter/@PoliceNG)
'Yan sandan Najeriya yayin kaddamar da rundunar wanzar da zaman lafiya a jihar Enugu.(Twitter/@PoliceNG)

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar dauke da sa hannun Kakakinta, SP Bala Elkana ta ce, an bi sahun ‘yan bindigar ne bayan kiran gaggawa da suka samu jim kadan bayan kisan Gulak.

Rahotanni daga jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya na cewa, jami’an ‘yan sanda sun kama tare da kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar da suka kashe Ahmed Ali Gulak, wadanda ta ayyana a matsayin mambobin haramtacciyar kungiyar IPOB ne.

An kashe Gulak, tsohon mai baiwa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara kan sha’anin siyasa a daren ranar Asabar a garin Owerri da ke jihar ta Imo, a lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama.

Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar dauke da sa hannun Kakakinta, SP Bala Elkana ta ce, an bi sahun ‘yan bindigar ne bayan kiran gaggawa da suka samu jim kadan bayan kisan Gulak.

Karin bayani akan: Ahmed Gulak, jihar Imo, Goodluck Jonathan, IPOB, Muryar Amurka, Nigeria, da Najeriya.

“'Yan kungiyar IPOB/ESN ne suka kashe Gulak,” in ji 'yan sandan jihar.

“An rutsa ‘yan bindigar ne a mahadar hanyar Afor Enyiogugu a karamar hukumar Aboh-Mbaise. An kuma tarar da su suna rabawa al’umar yankin albasa, daga wata babbar mota da suka kwace, wacce ta taso daga arewacin Najeriya.”

Rundunar ‘yan sandan jihar ta Imo ta ce, maharan suna hango jami’an tsaron, sai suka bude masu wuta.

“Nan take jami’anmu masu kwazo, su ma suka mayar masu da martani, inda shida daga cikin wadanda suka yi kisan da wasu hudu daga cikin mambobin kungiyar maharan, suka mutu. Sannan an kwato motoci uku daga cikin motoci hudu da suka kai harin da ya yi sanadin mutwar Gulak.”

Sanarwar ta kara da cewa, “bayanan da aka samu daga shaidu da kuma direban da ya tuka Gulak zuwa filin jirage, su suka taimaka wajen ba da cikakken kwatancen maharan da irin motocin da suka kai harin da su.”

A cewar Elkana, maharan sun yi aika-aikar ce da motoci kirar Toyota Camry 2005, Toyota Sienna 1998, Toyota Hilux da kuma wata Lexus RX 330.

Rundunar ‘yan sandan ta jihar Imo ta ce, ‘yan bindigar sun farfasa masu motocinsu masu sulke da harsashai amma ba su lalace ba.

Baya ga kashe maharan, jami’an tsaron sun ce sun kwato bindiga kirar AK-47 guda uku, karamar bindigar hannu guda daya, madaukin harsashin AK-47 guda biyar da harsashai 92 a ciki da kuma layu.

XS
SM
MD
LG