Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Kama Dubban Masu Zanga Zanga A Rasha


Police detain a man during a protest against the jailing of opposition leader Alexei Navalny in Khabarovsk, 6,100 kilometers (3,800 miles) east of Moscow, Russia, Saturday, Jan. 23, 2021. Authorities in Russia have taken measures to curb protests…
Police detain a man during a protest against the jailing of opposition leader Alexei Navalny in Khabarovsk, 6,100 kilometers (3,800 miles) east of Moscow, Russia, Saturday, Jan. 23, 2021. Authorities in Russia have taken measures to curb protests…

Dubun dubatan magoya bayan madugun ‘yan adawan Rasha da aka daure, Alexei Navalny sun dunguma a kan titunan Rasha a jiya Asabar, suka bijirewa kashedin hukumomi cewa duk wanda ya shiga zanga zangar ‘yan sanda zasu kama su kana akwai yiwuwar zasu kamuwa da coronavirus.

Navalny ne ya kira wannan zanga zangar bayan da aka kama shugaban ‘yan adawan yayin da isa Rasha daga kasar Jamus a karshen mako, inda ya fara murmurewa daga harin guba da aka kai masa da ya kusan hallaka shi.

Wata kungiyar sa ido mai zaman kanta, OVD-Info, ta ce an kama kimanin mazu zanga zanga dubu 3,200 da yammacin jiya Asabar, ciki har da matar Navalny, Yulia da hadimarta Lyubov Sobol, ‘yar siyasa.

Yulia Navalny ta tabbatar da kamata da aka yi a birnin Moscow a wani sako da ta kafe a shafin Instagram daga cikin motar ‘yan sanda, tana neman afuwa game da rashin ingancin sakon da ta kafe.

Ta ce “a yi hakuri da ingancin sakon. Babu isasshen haske a cikin motar ‘yan sandan,” ta rubuta a jiya Asabar.

Dubban magoya bayan Navalny sun gudanar da zanga zanga a cikin sama da garuruwan Rasha 60 a jiya Asabar domin neman mahukunta a Kremlin su gaggauta sakin shi, sun bijirewa matakan da ‘yan sanda suka dauka na hana zanga zangar da suka ira haramtacciya.

A Moscow, dubban masu zanga zanga saye da kyallen rufe huska sun taru a dandalin Pushkin Square a birnin suna ihu suna fadin “a kyale shi ya tafi” kana suna fadin “Alexei! Alexei.”

Masu zanga zangar sun rika kwalaye masu rubutu kamar “A baiwa Navalny ‘Yancinsa” kana “Bana tsoro.”

XS
SM
MD
LG