Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Sanda Sun Kashe Masu Zanga Zanga Biyu a Kenya


Masu ZangaZanga a Kenya

Akalla yan sanda sun kashe masu zanga zanga biyu a yau Juma’a a yammacin kasar Kenya yayin da suka kai samame a kan wata tashar yan sandan da makaman gona da duwatsu a cewar yan sandan.

Shugaban yan sandan Bondo Paul Kiarie yace an harbe wasu yan zanga zangar guda uku a kauyen Siaya amma ba a kashesu ba.

An gudanar da zanga zanga a yau Juma’a a babban birnin kasar Nairobi da Mombasa da kuma Kisumu. Yan sanda sunyi amfani da hayaki mai sa hawaye a kowane birni don tarwatsa masu zanga zangar.

A jiya Alhamis ministan harkokin cikin gida Fred Matiangi ya bada umarnin hana zanga zanga a wadannan birane, inda ya fito karara yace akwai hadarin fadawa cikin rashin zaman lafiya.

Duk biranen uku, wurare ne da madugun jami’iyar adawa Raila Odinga keda rinjayi wanda ya sance kansa daga zaben zagaye na biyu da za a yi a ranar 26 ga wannan watan Oktoba, saboda hukumar zaben kasar bata canza jami’anta da yake zarginsu da shirya magudi a zaben na farko.

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG