Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Belarus Sun Murkushe Masu Zanga Zanga A Minsk


Masu zanga zanga a Belarus
Masu zanga zanga a Belarus

‘Yan Sanda a birnin Minsk na kasar Belarus sun yi amfani da tankar ruwan zafi wajen tarwatsa taron jama’a yayin da ake ci gaba da zanga-zangar kin jinin shugaba Alexander Lukashenko a Lahadi ta tara a jere. A kalla mutane dubu 100,000 suka fito kan tituna a birnin a jiya Lahadi.

Tun da shugaban wanda ya dade akan mulki ya yi ikirarin lashe zaben da ake takaddama akai na tara ga watan Agusta, masu zanga-zanga suke fitowa tituna akai-akai suna neman da ya sauka kuma a saki fursunonin siyasa.

Lukashenko ya kafe akan shi ya lashe zaben da tazara mai yawa ta kashi tamanin cikin dari na kuri’un da aka kada, duk da zarge-zargen da ake ta yi a gida da wajen kasar na cewa an tafka magudi a zaben domin ya zarce kan mulki.

A karshen makon nan Belarus ta soke tantance ‘yan jaridar kasashen waje. A makon da ya gabata kuma kungiyar Tarayyar Turai wato EU, ta kakaba takunkumi akan jami’an Belarus kusan 40 da ake zargin su da sauya sakamakon zaben da kuma kame masu zanga-zanga.

Babu sunan Lukashenko a cikin jerin sunayen.

Fushin jama’a ya karu game da kamen na masu zanga-zanga inda aka kame fiye da mutane 7,500 da karuwar farmaki da ‘yan sanda suke kai musu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG