Accessibility links

'Yan sandan kasa da kasa na Interpol sun bada sammacin kama Gaddafi

  • Ibrahim Garba

Tsohon Shugaban Libiya Moammar Gaddafi

‘Yan sandan kasa da kasa na Interpol sun bayar da sammacin kama tsohon shugaban

‘Yan sandan kasa da kasa na Interpol sun bayar da sammacin kama tsohon shugaban Libiya Muammar Gaddafi bisa zargin aikata manyan laifuka na cin zarafin bil’adama.

A wata sanarwar da suka bayar a yau Jumma’a, ‘yan sandan na Interpol sun ce sun bayar da kwakkwaran sammacin kama Mr. Gaddafi, da dansa Saif al-Islam da wani tsohon shugaban hukumar leken asiri Abdullah al-Senussi, tare da kiran dukkannin kasashe 188 da ke ma’amala da Interpol din su taimaka wajen ganowa da kuma damke su.

Sakatare-Janar din Interpol Ronald Noble ya bayyana Mr. Gaddafi da cewa mai gudun kamu ne, y ace sammacin kama shin zai taimaka wajen takaita ketara kan iyakokin kasashen da ya kan iya.

Gaddafi, wanda har yanzu ba a san inda yak e ba, ya cigaba da boyewa tun bayan da dakarun da ke adawa da gwamnatin su ka abka cikin Tripoli, babban birnin ran 21 ga watan Agusta.

A jiya Alhamis, wani gidan talabijin din Syria ya saka muryar da aka ce ta Gaddafi ce, inda ya karyata rahotannin cewa watakila ya tsere daga kasar zuwa Janhuriyar Nijar das u ke makwabtaka. Mr Gaddafi ya ce har yanzu dakarunsa za su iya tinkarar dakarun Majalisar Shugabancin Wuccin Gadin, day a bayyanasu da cewa beraye ne, kwari kuma bata gari.

XS
SM
MD
LG