Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Malaysia Sun Kai Samame Gidan Tsohon Firayim Mministan Kasar


Mahathir Mohammed, sabon Firayim Ministan Malaysia

'Yan sandan Malaysia sun kai samame gidan tsohon Firayim Ministan kasar Najib Razak suna neman wasu takardu dake da alaka da binciken salwantar wasu kudaden saka jari

‘Yan sandan kasar Malaysia sun kai sumame gidan tsohon Prime Ministan kasar Najib Razak, da aka bada rahoton cewa suna neman wasu takardu, a zaman wani bangare na sabunta binciken abun fallasar cin hanci daya danganci kudin zuba jari na kasar.

An ga ‘yan sanda da yawa a gidan Najib jim kadan bayan ya dawo daga Sallah daga Masalacin dake kusa a jiya Laraba.

Galibi dai ne ke cewa an yiwa Najib daurin talata tun lokacida ya sha kaye a zaben da aka yi a makon jiya. Haka kuma an haramtawa Najib da matarsa fita zuwa wata kasar waje.

Shi dai Najib ya musunta zargin da ake yi masa. ‘Yan sandan kasar suna binciken wannan abun fallasar a akalla kasashen waje shidda ciki harda Amurka.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG