Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Siyasa Ne Suke Jefa Najeriya Cikin Matsaloli – Rochas


Rochas Okorocha (Facebook/Rochas Okorocha)
Rochas Okorocha (Facebook/Rochas Okorocha)

Tsohon gwamnan na jihar Imo ya ce dalilin da ya sa ‘yan siyasa ke haifarwa da Najeriya matsaloi shi ne, yadda ake bari kowa da kowa yake shiga harkar siyasa.

Tsohon gwamnan jihar Imo Chief Rochas Okorocha ya ce 'yan siyasar Najeriya suna taka gagarumar rawa game da barakar da ke wakana tsakanin kabilu da mabiya addini daban-daban na kasar, lamarin dake barazana ga makomar ci gaba da hadin kan al'umar kasar.

Okorocha ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta musamman da ya yi da Muryar Amurka.

“Ai dama, mu muka kawo damuwar da ake ciki a kasar nan, ‘yan siyasa ne ba kowa ba. In har muka yarda cewa ana so a samu hadin kan kasar nan ai zai yiwu.” In ji Okorocha.

Okorochas na magana ne kan taron daurin auren Yusuf Buhari, da ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da aka yi a garin Bichi na Jihar Kano a karshen makon jiya, inda ya ce yadda manyan ‘yan siyasa suka hada kai a wurin auren ya nuna a fili cewa, 'yan siyasar na iya magance matsalolin kasar da kansu.

Shugaba Buhari, Goodluck Jonathan, Atiku Abubakar a lokacin daurin auren Yusuf Buhari da Zahra (Facebook/Femi Adesina)
Shugaba Buhari, Goodluck Jonathan, Atiku Abubakar a lokacin daurin auren Yusuf Buhari da Zahra (Facebook/Femi Adesina)

Sai dai tsohon gwamnan na jihar Imo ya ce dalilin da ya sa ‘yan siyasa ke haifarwa da Najeriya matsaloi shi ne, yadda ake bari kowa da kowa yake shiga harkar siyasa.

“Wadanda bai kamata a ce suna siyasa ba suna siyasa, wasu siyasarsu ta kasuwanci ce ba siyasar al’umar ko ta kishin kasa ba, su dai a sa mu mulki a samu kudi, akwai su suna nan da yawa a kasar nan.”

“Sannan akwai wadanda siyasarsu ta kabilanci ce da addini, in ba addini ko kabilanci, su ba ruwansu, su ma suna nan da yawa a kasar nan .”

A cewar Okorocha, kalilan ne daga cikin ‘yan siyasar suka sa Najeriya a gabansu suke kishinta.

Rochas ya kuma ce ya ji dadi yadda ya ga shugabannin Najeriya suka hadu a wurin daurin auren dan shugaba Buhari yana mai cewa hakan zai kawo hadin kai a Kasar.

Manyan 'yan siyasan Najeriya a waken daurin Auren Yusuf Buhari da Zahra Nasir Ado Bayero (Facebook/Femi Adesina)
Manyan 'yan siyasan Najeriya a waken daurin Auren Yusuf Buhari da Zahra Nasir Ado Bayero (Facebook/Femi Adesina)

“Najeriya ta hadu, da wadanda ma ban yi tsammanin za su je ba, da wadanda da ba sa shiri da shugaban kasa duk sun zo, irin wannan taro yakan kawo hadin kai.” Rochas ya ce.

Duarin auren dan shugaban kasar ya tattaro manyan ‘yan siyasan Najeriya daga jami’yya mai mulki ta APC da bangaren jam’iyyar adawa ta PDP, wadanda suka hada tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Fani-kayode da Alhaji Buba Galadima.

Saurari cikakkiyar hirar da Rochas Okorocha:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:34 0:00


XS
SM
MD
LG