Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Harin Kwantan Bauna Ya Kashe Sojoji 17 A Jamhuriyar Nijer


Dakarun Jamhuriyar Nijer

Wani kakakin gwamnatin Jamhuriyar Nijar yace an kashe a kalla sojoji goma sha bakwai yayin da wadansu goma sha daya kuma suka bace bayan da wadansu mahara da ba a san ko su wanene ba suka yi masu kwantan bauna.

An kai harin ne a kauyen Tongo Tongo dake yammacin Nijar. Kauyen yana lardin Tillaberi inda mahara suka kashe dakarun sojin Amurka hudu da na jamhuriyar Nijar hudu a shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai.

Wani jami’in tsaro ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa cewa, ana kyautata zaton kwantan baunan da aka kai ranar Talatan harin ta’addanci ne.

Wata kungiyar da ake alakantawa da kungiyar IS ta dauki alhakin harin da aka kai a shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG