Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sudan Sun Yi Gagarumar Zanga Zanga Kan Tabarbarewar Rayuwa


Zanga zanga a Sudan
Zanga zanga a Sudan

A jiya Asabar dubban masu zanga zanga a Sudan sun hau tituna a babban birnin kasar Khartoum da birni na biyu Omdurman suna neman a gaggauta sauye sauye a kasar yayin da ake cika shekaru biyu da boren da ya hambarar da shugaba Omar al-Bashir daga mulki.

An hambarar da dadadden shugaban kasar ne a wani juyin mulkin soji a cikin watan Afrilu a shekarar 2019, bayan gagaruman zanga zanga a kan tabarbarewar tattalin arziki da kuma mulkin kama karya da Bashir ya yi a mulkin sa na shekaru 30.

Galibin ‘yan Sudan sun bayyana rashin jin dadin su a kan abin da suka kira tafiyar hawainiya ko kuma sauya tafiya da ake gani karkashin gwamnatin wucin gadi da ta sha fama wurin magance matsalolin tattalin arziki a lokaci da kasar take cikin rikici.

An kafa gwamnatin ne a karkashin yarjejeniyar shekaru uku ta raba madafun iko tsakanin sojoji da kundiyoyin fararen hula, da zummar zata shirya zaben gaskiya na shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki.

Telbijin gwamnatin Sudan ta nuna hoton dubban masu zanga zanga sun taru a wajen fadar shugaban kasa a birnin Khartoum, inda hukumar zartarwar kasar ke gudanar da ayyukanta karkashin gwamnatin hadaka tsakanin sojoji da fararen hula.

An kashe daruruwan ‘yan Sudan a cikin zanga zanga kafi hambarar da tsohon shugaban kasar da ma bayan da ya sauka daga karagar mulki.

Wasu da dama suna kira ga rusar da majalisar dokoki da ta zartarwar da kuma gwamnatin hadakar.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG