Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

MDD Ta Kara Kaimi Wurin Neman Shiga Da Kayayyakin Jin Kai A Tigray


Yara a yankin Tigray
Yara a yankin Tigray

Sama da kananan yara miliyan biyu a yankin Tigray na kasar Habasha ne aka yanke su daga samun taimakon kayayyakin jin kai sama da wata guda, a cewar Majalisar Dinkin Duniya (MDD) a jiya Talata.

Muna matukar damuwa saboda idan aka ci gaba jinkirin isa gare su, zasu kara shiga cikin mummunar hali na rashin samun abinci kamar irin abinci dake taimakon yara masu tamowa da rashin magunguna da ruwa da mai da wasu muhimman abubuwan rayuwa da suka yi karanci a wurin, inji darektan asusun kananan yara na MDD wato UNICEF, Henrietta Fore, a wata sanarwa da ta rubuta jiya Talata.

Fore ta ce MDD ta shirya tsaf ta kai kayyaki da ayyuka da ake bukata na jinyar masu fama da tamowa a yankin da ake gwabza yaki amma tana buakatar izinin shiga Tigray da yanzu Addis Ababa ke hanawa.

An yake hanyoyin sadarwa kana an takaita shiga yankin na Tigray, tun lokacin da rikicin ya barke a ranar hudu ga watan Nuwamba, lamarin ya hana hukumomin jinkai kimanta buakatar da ake da ita a wurin.

Tigray dake arewacin Habasha kuma daya daga cikin yakuna tara a kasar, ya yi taurin kai ya shirya zabe a cikin watan Satumba, inda Debretsion Gebremichael ya lashe zaben, duk da shawarar da Firai Minista Abiy Ahmed ya yanke ta dakatar da zaben, saboda annobar coronavirus.

Gwamnatin Habasha ta kaddamar da ayyukan soja a kan Tigray bayan da dakarun yankin suka kai hari a kan tungar sojojin tarayya a cikin wata Nuwamba, a cewar Abiy. Abiy ya ce gwamnati tana kallon gwamnatin yankin karkashin jagorancin kungiyar Tigray People’s Liberation Front, TPLF haramtacciya. TPL ta musunta kai harin.

Tun a cikin watan Nuwamba, sama da mutum dubu 50 suka arcewa tashin hankalin na Tigray kana suka nufi kasar Sudan.

XS
SM
MD
LG