Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ta'adda Sun Yi Ma Wasu Mutane Yankar Rago A Maiduguri


An yi jana'izar wasu mutane da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka yi musu yankar rago a Maiduguri.

Wasu rahotanni dake fitowa daga yankin kudancin jihar Borno, na bayyana cewa, wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne, sun yiwa wasu mutane 8 yankar rago, a dai-dai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa neman itace.

Rahotannin dai sun kara da cewar mutanen suna zaune ne a cikin sansanin 'yan gudun hijira da ke yankin, wasu mutane da ke yankin sun tabbaara da aukuwar lamarin da cewar: Mutanen, wadanda har yanzu ba a san inda hudu daga cikinsu su ke ba, sun fita da safe ne don neman itace, koda aka duba bayan gari an yi musu yankar rago, kimanin kwanaki 6 da suka wuce, an dai yi jana'izar su a ranar Juma'a.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu, daga Maiduguri a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:42 0:00

Karin bayani akan: Maiduguri​, Boko Haram, jihar Borno, Nigeria, da Najeriya.

Dubi ra’ayoyi

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto

Yaran Da Boko Haram ta Kashe Iyayensu Sun Samu Gata a Sokoto
please wait

No media source currently available

0:00 0:05:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni – Dan Kasuwar Gwari A Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG