Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Sako Mutane 53 A Jihar Naija; Ban Da Daliban Kagara


Makarantar Sakandare ta Kagara
Makarantar Sakandare ta Kagara

‘Yan bindiga sun saki mutane 53 da suka sace a jihar Naija da ke Arewacin Najeriya, to amma ban da dalibai 27 na makarantar sakandare ta Kagara, da wasu murtane 15 da aka yi awon gaba da su a makon jiya.

Babbar sakatariyar hulda da ‘yan jarida ta gwamnan jihar Naija Mary Berje, a wata sanarwa ta ce an sako mutanen ne a daren jiya wayewar garin yau Litinin.

Sun hada da mutane 39 ragowar mutane 47 da ke cikin motar kamfanin sufuri na jihar, wadanda aka dauke su kafin daliban Kagara. Da ma can an sako mutane 8 daga cikinsu.

An hannunta mutanen da aka saki ne ga jami’an gwamnatin jihar, a wani wuri da ba’a bayyana ba a cikin jihar Zamfara.

Jaridar THISDAY ta Najeriya ta ruwaito Sakataren Gwamnatin jihar ta Naija Alhaji Ahmed Matane, yana cewa masu garkuwa da daliban ba su nemi kudin fansa ba, to amma ana nan ana tattaunawa da su domin sako daliban.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an gwamnatin jihar sun isa garin Kagara tun a daren Lahadi, suna jiran sako mutanen da aka yi garkuwa da su.

Makarantar Sakandare ta Kagara
Makarantar Sakandare ta Kagara

Sakin mutanen 53, ya haifar da kwarin gwiwa da sa ran cewa za’a sako daliban da malamansu a yau Litinin.

Wasu rahotanni kuma na bayyana cewa sakin mutanen, da kuma kokarin ganin an sako daliban Kagara, duk sun gudana ne ta hanyar sulhu a karkashin jagorancin malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gummi.

XS
SM
MD
LG