Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Libiya Sun Tsere Daga Brega


'Yan tawayen Libiya kenan ke yin ta kansu a sa'ilinda dakarun Gaddafi ke zafafa hare-hare a kansu.

Sojoji masu yin biyayya ga shugaba Muammar Gaddafi na Libya sun yi barin wuta a kan wuraren da ‘yan tawaye suka ja daga a kusa da garin Brega mai muhimmanci a harkokin man fetur a gabashin kasar, abinda ya sa mayakan ‘yan tawayen suka yi janyewa mafi girma a cikin kwanakin da aka shafe ana kiki-kaka kan wannan garin.

Sojoji masu yin biyayya ga shugaba Muammar Gaddafi na Libya sun yi barin wuta a kan wuraren da ‘yan tawaye suka ja daga a kusa da garin Brega mai muhimmanci a harkokin man fetur a gabashin kasar, abinda ya sa mayakan ‘yan tawayen suka yi janyewa mafi girma a cikin kwanakin da aka shafe ana kiki-kaka kan wannan garin.

Mayaka masu adawa da gwamnati sun janye daga Brega suka auna gabas domin komawa garin Ajdabiya, a saboda barin wuta na kwanson bam da rokokin da mayakan Gaddafi suka yi ta cilla musu. Sassan biyu sun yi musanyar wuta da manyan makamai jiya talata, kwana guda a bayan da ‘yan tawaye suka mamaye wata unguwa a garin.

Mayakan Gaddafi sun samu wannan nasara ce a daidai lokacin da madugun mayakan adawa na Libya ya fito da kakkausar harshe yana suka lamirin NATO a saboda ta kasa gudanar da aikinta na kare fararen hula. Jiya talata Abdel Fattah Younes ya zargi NATO da laifin nuna ragwancin zuciya tare da jinkiri wajen kai hare-haren da aka bukata daga sama a yayin da sojojin Gaddafi ke kashe mutanen birnin Misrata a yammacin kasar.

Yace ana samun jinkirin har awa 10 daga lokacin da ‘yan tawaye suka bukaci a kai farmaki kan wata cibiya kafin a aiwatar da hakan. Younes yace NATO ta ki yarda ta ba su izni a duk lokacin da suka bukaci yin amfani da jiragen saman yakinsu domin tallafawa sojojinsu na kasa. Yace zai bukaci shugabannin ‘yan tawayen da su kai kukarsu gaban Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya bayarda iznin yin amfani da karfi domin hana sojojin gwamnati kai farmaki kan fararen hula. Jami’an NATO sun ce ba su sassauto da sintirin jiragen saman yaki a kan Libya ba, amma Gaddafi ya samu dabarar boye manyan makamansa a tsakiyar fararen hula.

XS
SM
MD
LG