Accessibility links

'Yan Tawayen Libya Sun kashe Babban kwamandansu

  • Aliyu Imam

Shugaban majalisar 'yan tawayen Libya Mustafa Abdel Jalil

Majalisar gudanarwa ta ‘yan tawaye a Libya ta bada labarin wasu mahara dauke da makamaki, sun harbe suka kashe kwamandanta Abdel Fattah Younes, da wasu hadimansa biyu.

Majalisar gudanarwa ta ‘yan tawaye a Libya ta bada labarin wasu mahara dauke da makamai, sun harbe suka kashe kwamandanta Abdel Fattah Younes, da wasu hadimansa biyu.

Shugaban majalisar gwamnatin ‘yan tawayen Mustafa Abdel Jalil, ya fada jiya alhamis cewa, Younes da hadimansa biyu dukkansu masu mukamin kanal an kashe su gabannin su bayyana gaban wani kwamitin shari’a na ‘yan tawaye dangane da lamari na soja.

Yace an kama madugun reshen ‘yan tawaye da suka kashe su.

Jalil bai fito fili ya fadi wadda yake zargi da kashe Younes ba.Duk da haka ya yi kira ga dakarun ‘yan tawaye su yi watsi da kokarin gwamnatin Moammar Gadhafi na raba kawunansu. Haka kuma yayi gargadi ga wasu ‘yan banga dauke da makamai a wasu birane da suke karkashin ‘yan tawaye, cewa su shiga sahun yaki da Gadhafi, ko kuma a kamasu.

Sao’I kamin nan, ‘yan tawaye sun bada labarin sun tsare Younes, sabo da zargin da ake masa cewa har yanzu danginsa suna ci gaba da cudanya da wasu na hanun daman Gadhafi.

Younes ya juma yana ministan harkokin cikin gida a gwamnatinn Gadhafi, kuma na hanun daman shugaban ne, kamin ba zato ba tsammani ya sake sheka zuwa bangaren ‘yan tawaye da barkewar zanga zanga cikin watan febwairu. Yana daga cikin gungun mutane da suka yi juyin mulkin 1969 da ya kafa gwamnatin Gadhafi.

Jalil ya kira Younes “daya daga cikin jaruman juyin juya hali na 17 ga watan Febwairu”. Yace ‘yan tawayen zasu ayyana zaman makoki na kwana uku, tareda alwashin dakarun ‘yan tawaye zasu ci gaba da fafutukar hambare gwamnatin Gadhafi.

XS
SM
MD
LG