Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Wasan Rasha Ba Zasu Buga Gasar Nakasassu A Olympic Ba


Yan Wasan Rasha a Brazil

An dakatar da daukacin 'yan tawagar Rasha a gasar kasa da kasa ta Olympic na nakasassu, wadda za a yi a watan Satumba, a matsayin hukuncin da aka yanke ma kasar saboda amfani da kwayoyi masu kara kuzari.

Wanda 'yan wasan Rasha su ka yi ta yi, wanda ya zarce hukuncin rage ma kasar yawan shiga gasar guje-guje da tsalle-tsalle na lokacin bazarar "summer," wadda ake yi a Rio de Janeiro.

Kwamitin Gasar Olympic ta Kasa da Kasa ya amince da shigar 'yan wasan Rasha 271 a gasar ta Rio, wadanda kashi 70% na 'yan wasan kasar kenan.

To amma Kwamitin Gasar Kasa Da Kasa Na Nakasassun ya yi tir yadda 'yan wasan Rasha su ka yi ta amfani da kwayoyin kara kuzarin, ciki har da lokacin gasar kasa da kasa ta nakasassu wadda aka yi a Sochi na kasar ta Rasha a 2014, sannan ta hana 'yan wasan Rasha shiga gasar da za a yi daga 7 zuwa 18 na watan Satumba, wadda ita ma za a yi a Rio.

Bidiyo

Mijin Aljana A Kano: Shin Dama Aljanu Na Da ATM’ Na Kudi?
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG