Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Yawan Shakatawa 32 Sun Rasa Ransu a Hadarin Mota


Hadarin mota a Taiwan

Wata mota kirar bus dauke da ‘yan yawon shakatawar Taiwan ta yi hadari, inda ta halaka mutane 32 bayan da ta kife a hadarin da aka dade ba a gani ba cikin shekaru da dama.

‘Yan sanda sun ce bus din na dauke ne da fasinjoji 44, wadanda mafi yawansu sun manyanta, a lokacin da motar ta kife a yammacin jiya Litinin a wata babbar hanya dake Taipei, babban birnin Taiwan.

Jami’a sun ce mutane 12 na karbar magani a asibiti, kuma da yawa daga cikinsu suna dauke da munanan raunuka.

Wani hoton bidiyo da motar da ke bayan bus din ta dauka, ya nuna yadda bus din ta kife ta kuma zame yayin da take kokarin shan wata kwana.

Hukumomin a Taiwan sun ce suna kokarin su gano abin da ya haddasa hadarin tare da yin dubi ko motar na dan-karan gudu ne.

Wani hadarin mota da aka yi a bara ya halaka wasu ‘yan yawon shakatarwar China su 24.

XS
SM
MD
LG