Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Sandan Kwantar Sun Tarwatsa masu zanga zanga a Belgium


Police look at bags of evidence material during a search in the Brussels borough of Schaerbeek following Tuesday's bombings in Brussels, Belgium, March 25, 2016.
Police look at bags of evidence material during a search in the Brussels borough of Schaerbeek following Tuesday's bombings in Brussels, Belgium, March 25, 2016.

Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi amfani da motocinsu na feshin ruwa suka kutsa cikin masu zanga-zanga a Belgium da suka yi dandazo da nufin tarwatsasu.

Masu zanga-zangar da suka bayyana a daidai lokacin da jama’a ke makokin wadanda suka mutu a harin da aka kai na filin jirgin saman Brussels a makon da ya gabata.

‘Yan zanga-zangar da akewa lakabi da Right-wing, sun bayyana suna rera wakokin kin jinin karbar bakin ketare, da alamta sarawar ko kamewa irin ta ‘yan Nazi.

Wani Mai Sana’ar yin gidaje Monique Starck yace, “sun saba bayyana da wannan sigar ta sake dagula lamari, matukar akwai wani babban al’amari makamancin haka a kasa”.

Tun dai faruwar lamarin da ya hallaka akalla mutane 28, jama’a suke wannan dandali don nuna jimami ga mamatan da abin ya ritsa da su.

Wadannan mutane da ke da’awar cewa su ‘yan tsiraru ne masu adawa da ta’addanci, suna isowa sai naushe-naushe tsakaninsu da masu makokin.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG